12 Yuni 2017 - 15:44
Jami’an tsaro Iran Sun Hallaka Wasu ‘yan Ta’adda 4

Jami'an tsaron Iran sun bada sanarwar hallaka wasu ‘yan ta'adda guda 4 a garin Ruan dake yankin Hurmuzgan, an samu ‘yan ta'adda dauke da 4 da alburusai 112 da kuma wasu abubuwa masu fashewa.

Kamfanin dillancin labarai

Daesh

Daesh

na Ahlul-Baiti (a.s)-abna-ya rawaito shugaban ‘yan sandan yakin Hurmuzgan Azizullahi a yayin da yake jawabi gaban manema labarai cewa; rudunar tsaron yakin sunyi nasarar murkushe ‘yan ta’adda dake gabacin jahar ta Hurmuzgan inda suka hallaka mutane hudu ya kuma kara da cewa biyu daga cikinsu ‘yan wasu kasashe ne sai dai ya boye suna kasashe
Azizullahi ya kara da cewa: a binciken da suka yi sun samu mutane dauke da bindigogi 4 da alburusai 112 sai kuma wasu ababai masu fashewa.
Daga karshe ya ba al’ummar kasar tabbacin kawo zaman lafiya da kuma sa kafar wando daya da duk wani asharari